1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayar wa Fulani burtalai a fadin jihar Jigawa

August 13, 2019

Gwamnatin jihar Jigawa ta dau hanyar kawo karshen rikicin da aka dade ana yi na makiyaya da manoma inda ta ba da umarnin a mayar musu da burtalansu da manyan 'yan siyasa suka kwace.

Nigreria Fulani-Nomaden
Hoto: AFP/Luis Tato

Gwamnan jihar Jigawa da ke Najeriya Alhaji Badaru Abubakar shi ne ya bayar da umarnin gaggauta mayar wa da Fulani burtalansu da aka karbe ake nomawa domin su sami wajen kiwata dabbobinsu. A cewar gwamnan babu dan jam'iyya babu wanda ba dan jam'iyya ba a lamarin, domin kuwa duk 'yan jihar Jigawa ne suka zabe shi a matsayin gwamnansu.


Jama'a da yawa dai na hangen cewa wannan matakin na gwamnan zai taimaka wajen magance matsalar baki daya a jihar, kuma Fulani da dama sun yi murna da wannan mataki. Sai dai Fulanin sun kara da yin gargadi ga jama'a da su bi wannan umarnin na gwamna sau da kafa domin wanzar da zaman lafiya, sun kara da cewa duk mutumin da ke karkashin shugabanci ya zama tilas ya bi umarnin gwamnati ya kuma bi doka domin babu wanda yafi karfin doka ta hau kansa. Fulanin sun kara da lasar takobin sanar da gwamna jihar ta Jigawa labarin duk wanda bai bi wannan umarni ba. Sun yi kuma kira ga 'yan uwansu Fulani da su kara kiyayewa, su daina daukar doka a hannunsu, duk wanda yake ganin an zalunce shi, sai ya kai kukansa ga shugabanninsu na gargajiya.

Hoto: DW/K. Gänsler


Sai dai masana na ganin cewar wannan matakin na gwamnan ka iya janyo wata sabuwar matsalar daga dadadden rikicin.  Wani mazaunin garin Gumel Ahmad Muhammad Gumel ya yaba wa gwamnati a kan matakin da ta dauka ya na mai cewa wannan alama ce da ke nuni da cewar gwamnan yana da karfin ikon kujerarsa kenan da ya dauki irin wannan mataki.


Daga bangaren manoman kuma wani wanda yake magana da yawunsu ya ce sun sami wannan labari ya zo musu da abu biyu; farin ciki da bakin ciki, domin a da suna murna suna da wadataccen wurin da za su yi noma, amma yanzu zuwan wannan umarnin na gwamna ya maida da hannun agogo baya. To amma kuma dole su bi wannan umarni.