Jigilar jirage ta soma tsayawa a Afirka
March 21, 2020Talla
Kamfanin jiragen kasar Afirka ta Kudu na daga cikin kamfanonin da suka sanar da daukar wannan matakin na dakatar da zirga-zirga.
Haka nan kamfanin Ethiopian Airlines wanda ya fi kowanne karfi a harkokin sufurin sama a nahiyar, ya sanar da soke jigila zuwa kasashe 30.
Dama dai an dauki lokaci ana zargin kamfanin na Ethiopian Airlines, da sanya nahiyar Afirka cikin hadarin wannan cuta, saboda ci gaba da ya yi da jigila zuwa kasashen da cutar ta yi kamari a cikin su, musamman ma kasar China inda wannan cuta ta samo asali.
A yanzu dai kasar Afirka ta Kudu ce ke kan gaba a Afirkar da yawan mutum 202 da suka kamu da cutar sarkewar numfashin ta COVID-19.