1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jigon adawa a Kwango ya kulla kawance da 'yan tawaye

December 16, 2023

Wani jigon dan adawar Kwango da ke zaman hijira, ya sanar da kafa wata kungiyar siyasa mai kawance da kungiyar tawaye ta M23 da ma wasu kungiyoyi masu gaba da gwamnati.

Hoto: Luis Tato/AFP

Wannan hadakar da dan siyasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Corneille Nangaa ya sanar, ta sanya gwamnatin Shugaba Felix Tschekedi gargadin kasar Kenya da ke ba shi mafaka.

Yayin sanar da sabuwar kawancen dai, an ga jigon na adawa Nangaa tsaye da jagoran tawayen Kwangon Betrand Bisimwa a wani Otel da ke birnin Nairobi.

Batutuwa na siyasa da tsaro dai na ci gaba da kara dumi a Jamhuriyar Dimkuradiyyar Kwango, gabanin zaben da za a yi a ranar 20 ga wannan wata na Disamba.

Zabe ne dai da Shugaba Felix Tschekedi mai shekaru 60 da ya hau karagar mulki a 2019, ke neman a sake zaben sa a karo na biyu.