1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jihohi 30 na fuskantar barazanar ambaliya a Najeriya

Zainab Mohammed Abubakar
April 11, 2025

Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta Najeriya ta yi gargadin cewa, jihohi 30 da Abuja hedikwatara kasar za su fuskanci ambaliyar ruwa a wannan shekarar.

Hoto: Uwais Idris/DW

Wannan gargadi da ma jan hankali na a shirya wa yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa a jihohi 30 da Abuja da ma'aikatar kula da albarkatun ruwa da tsaftace muhalli ta fitar ya nuna irin gimrman barazanar da za'a fusknata. Domin kuwa alummu 1,249 a kanana hukumomi 176 ne aka hango za su fuskanci bala'in ambaliyara ruwan a daminar bana.

An dai kasa barazanar zuwa sassan uku da wadanda ke gabar teku da wuraren da za'a iya fuskantara ambaliyar ruwan saboda rashin magudanan ruwa masu kyau da sauran wurare. Wannan zai raba mutanen da dama daga muhallansu musamman wadanda ke zaune a kusa da gabar rafuka da koguna a kasar baya ga lalata amfanin gona. Farfesas Joseph Utsev shi ne ministan albarkatun ruwa da tsaftace muhalli na Najeriyar da ya bayyana dalilin da zai sa afkuwar ambaliyar ruwan.

Saboda matsala ta tumbatsa da cikar da rafuka za su yi da sauran ayyuka na bani adama a gandun daji jihohin za su fukanci matsalar da suka hada da Bayelsa da Cross River da Delta da Lagos da Ogun da Rivers da kuma Ondo za su fukanci ambaliyar ruwa ta gabar teku.

Tun kafin wannan gargadi dai an fara ganin alamun yadda daminar zata kasance inda a Abuja hedikwatar Najeriya ruwan saman da aka yi sau biyu ya haifar da ambaliyar ruwa a wasu sassan birnin duk kuwa da kyawawan magudanan ruwa da ake da su a birnin wanda bama a gabar teku ko wani rafi yake ba.

Ba kamar lokutan bay aba, a wannan karon an samu hasashen zahirin alamun da ambaliyar ruwan zata iya fusknata. A shekararar da ta gabata dai balain ambaliyar ruwa ya yi mumunan illa a jihohi da daman a Najeriyar, domin bayani sun nuna cewa mutane 321 ne suka mutu yayainda fiye da mutane 1,300 ambaliyar ruwan ta shafa.

Barazanr ambaliyar ruwa a bana na tada hankali saboda matsalar karancin abinci da hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ‘yan Najeriya sama da milyan 30 ne ke fuskantar barazanar karancin abinci. A ko-wace shekara a kan fitar da irin wannan gargadi na barazanar ambaliyar ruwa amma kama daga jama'a zuwa gwamnati haka a kan bar lamari sai ya faru a fara kame-kame.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani