1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jimami: Shekaru 30 da kisan kiyashi a Rwanda

Abdullahi Tanko Bala
April 7, 2024

Ranar 7 ga watan Afrilu aka cika shekaru 30 da kisan kiyashi a Rwanda inda aka hallaka mutane kusan miliyan daya 'yan Tutsi da 'yan Hutu masu sassaucin ra'ayi a shekarar 1994. Har yanzu al'umma na cikin alhini da jimami

Tuna mutanen da suka rasu a kisan kiyashi a Rwanda
Tuna mutanen da suka rasu a kisan kiyashi a RwandaHoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Mutane kusan miliyan daya ne dai yawancinsu 'yan kabilar Tutsi marasa rinjaye da kuma wasu kalilan 'yan Hutu masu sassaucin ra'ayi da ke zama mafi rinjaye da suka yi kokarin bada kariya ga 'yan Tutsi aka hallaka. 'Yan kabilar Hutu wadanda su ne mafiya rinjaye a kasar  suka aikata ta'asar kisan gillar cikin kwanaki 100. Lamarin ya fara ne a ranar 7 ga watan Afrilun 1994.

Majalisar Dinkin Duniya na zama na musamman domin karrama mutanen da suka tsira daga wannan ta'asa.

Tuna kisan kiyashi a Rwanda shekaru 30 da suka wuceHoto: Sayyid Abdul Azim/AP/picture alliance

A cikin wata sanarwa sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ba za a taba mantawa da mutanen da wannan bala'i na kisan kare dangi ya shafa ba. Haka kuma ba za a manta da irin bajinta da juriyar da suka nuna ba.

Freddy Mutanguha, dan Tutsi ne, kuma yana daga cikin mutanen da suka tsira.

Karin Bayani: Macron ya nemi afuwan Ruwanda kan kisan kiyashi

"Ya ce ina iya tunawa ina ji yan uwana suna kuka yayin da ake yi musu kisan rashin imani. Suna rokon maharan su yi musu rai amma a banza. Sun jefa yan uwana mata cikin wani rami da ke kusa, wasu da ransu amma sai suka karasa su da buga musu duwatsu. Iyayena kuwa sun hallaka ne da adduna"

Shekarun Freddy 18 a lokacin kisan kiyashin kuma ya je kauyensu ne Mushubati da ke Kibuye mai tazarar kilomita 135 Kigali babban birnin Rwanda bayan samun hutun makaranta.

'Yan Hutu masu tsattsauran ra'ayi sun rika farautar matasa maza wadanda suke zargi da tausaya wa ko nuna goyon baya ga kungiyar kishin kasa ta Rwanda wato Rwanda Patriotic Front (RFP) wadda kungiya ce ta galibi yan Tutsi karkashin jagorancin Paul Kagame wanda ya zama shugaban kasar Rwanda.

Shugaban kasar Rwanda Paul KagameHoto: Halil Sagirkaya/Anadolu/picture alliance

Bayan rasa iyayensa da yan uwansa mata su hudu, Freddy ya kuma rasa danginsa su kimanin 80 a kisan gillar.

Wasu daga cikin wadanda suka kashe dangin Freddy, an sako su daga gidan yari a karkashin wata yarjejeniya cewa za a yi afuwa ga wadanda suka yi zaman gidan yari na rabin wa'adin da aka yanke musu idan suka bayar da bayanai ga masu gabatar da kara game da wandanda ake zargi da kuma inda aka jefar da gawarwakin mutanen da aka kashe. Sai dai jigajigan wannan ta'asa har yanzu suna nan a gidan yari.

Karin Bayani: Shekaru 20 da kisan kiyashi a Ruwanda

Freddy, wanda tsohon mataimakin shugaban kungiyar IBUKA ne, kungiyar wadanda suka tsira daga kisan kiyashin Rwanda, yanzu shi ne daraktan gidan tarihin Kigali na kisan kiyashi inda aka binne gawarwakin mutane 250,000 da aka yiwa kisan gillar.

Duk da kokarin Rwanda na sasanta tsakanin mutanen da suika tsira da kuma wadanda suka aikata kisan kiyashin, lamarin na cigaba da sosa ran wasu da suka tsira kamar Freddy da 'yar uwarsa Rosette.

Ya ce wadanda suka aikata wannan abu ba kasafai suke baiyana dukkan gaskiyar ba, wanda hakan shi ne yake kawo cikas ga kokarin sasantawa, abin kuma da ya ke damun wadanda suka tsira. Yana mai cewa daya daga cikin wadanda suka kashe danginsa ya boye bayanai da dama.

Tuna kisan kiyashi na 1994 a RwandaHoto: Sayyid Azim/AP Photo/picture alliance

"Ya ce an sake shi bayan da ya yi shekaru 15 a gidan yari maimakon shekaru 25 da aka yanke masa, saboda kawai dan bayanan da ya bai wa masu gabatar da kara. To amma haka muke rayuwa tun da babu yadda za mu yi, wadanda muka rasa ba za a iya dawo da su ba."

Sai dai kuma Freddy ya amince cewa gwamnatin Rwanda ta sami gagarumar nasara wajen sasantawa.

Farfesa Phil Clark masanin siyasar duniya a sashen nazarin harsuna da al'adun gabashin Afirka (SOAS) da ke Jami'ar London  ya yi tsokaci kan batun yana mai cewa:-

"Ya ce a fahimta ta tsawon shekaru ashirin da na yi ina bincike a Rwanda, ina ganin akida ta kisan kare dangi ta ragu matuka."

Clark ya ce babban kalubale na sasantawa a Rwanda a yanzu shi ne yan Rwanda da ke kasashen waje  wadanda su  ne har yanzu basu shiga cikin shirin sasantawa a cikin kasar ba. Su ne kuma suke yada bayanan da ke raba kawuna a shafukan sada zumunta ga danginsu da ke gida wanda hakan ke kawo cikas ga yunkurin sasantawar musamman a tsakanin matasa wadanda basu da masaniya sosai a kan abin da ya faru shekaru 30 da suka wuce.

Tuna baya na abin da ya faru a Rwanda shekaru 30 da suka wuce ba abu ne yan Tutsi kadai da suka tsira daga kisan kare dangi ba amma lamari ne da duniya baki daya za ta yi koyi daga gare shi saboda laifi ne da aka aikata kan bil Adama.

Karin Bayani: