1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jin ba'asi kan shirin tsige Shugaba Trump

Ahmed Salisu
November 13, 2019

Nan gaba a yau ne za a fara sauraron ba'asi daga shaidu kan shirin majalisar dokokin Amirka na tsige shugaban kasar Donald Trump, inda rahotanni ke cewar za a nuna yadda zama zai wakana a gidajen talabijin.

US-Präsident Donald Trump
Hoto: Getty Images/AFP/B. Smialowski

Rahotanni daga Amirka na cewar za a fara sauraron ba'asin wasu manyan jami'an diflomassiyar Amirka wadanda suka hada da William Taylor wanda yanzu yake aiki a ofishin jakadancin Amirka a kasar Ukraine da kuma George Kent da ke zaman mukaddashin sakatare mai kula da huldar Amirka da kasashen Turai.

Zaman na wannan rana dai zai mayar da hankali ne wajen jin ta bakin Mr. Taylor da Mr. Kent dangane da zargin da ake yi wa shugaban na Amirka wajen amfani da manufofi na kasashen waje don cimma burinsa na siyasa gabannin zaben shugaban kasa a shekarar 2020.