Jirage za su fara aiki a tsbirin Bali
November 30, 2017Talla
An samu sauyin shekar iska da ya rage tudun toka da hayaki a filin jirgin, aman wutar duwatsun Agung ya haifar da tarin toka da ke zama barana ga lafiyar jiragen sama wanda ya yi sanadiyar cunkushe masu yawon bude ido akalla dubu 120 tun bayan faruwar al'amarin a ranar Litinin.
A shekarar 1963 an samu aman wuta a yankin na Bali mai keweye da tsaunuka wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu daya. Duk dai da cewa a wannan karon babu asarar rai, mazauna yankin Bali sun kauracewa gidajensu don gudun sake fashewar duwatsu.