Jiragen Jamus sun shiga yaki da Kungiyar IS
December 16, 2015Talla
A karo na farko wani jirgin sojojin kasar Jamus ya shiga an dama da shi a yakin da rundunar kawance kasanshen duniya ke yi da Kungiyar IS.
Wani kakakin rundunar sojin samar kasar ta Jamus ta Bundeswehr ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa Jirgin samfarin A310 MRT ya gudanar da aikin bayar da mai a sararin samaniya ga wasu jiragen yaki rundunar kawancan a cikin daren Talata washe garin laraba .
A farkon wannan wata na Disamba ne dai majalisar dokokin Jamus ta bai wa kasar izinin bai wa rundunar kawancan kasashen duniyar mai yaki da kungiyar IS gudummawar sojojin dubu da 200 da jiragen yaki shida sanfarin tornado da kuma masu aikin bayar da mai ga jiragen yaki a sararin samaniya.