Jiragen kasa a Jamus zasu koma aiki
November 7, 2014Wannan yajin aiki da aka shirya tun da fari za a kammala a ranar Litinin, na zuwa ne adaidai lokacin da ake shiga ruguntsumin bikin tunawa da ranar faduwar katangar Berlin karo na 25 a karshen mako.
Claus Weselsky da ke zama jagoran kungiyar direbobin jiragen kasan na Deutsche Bahn, ya bayyana cewa za a kawo karshen yajin aikin ne a ranar Asabar da misalin karfe shida na yammaci, hakan kuwa na zuwa ne bayan da kotu ta yi watsi da karar da kamfanin dake lura da harkokin safarar jiragen kasar na Jamus Deutsche Bahn na cewa yajin aikin da direbobin suka shiga baya bisa ka'ida.
Wannan yajin aikin dai, ya tsaida zirga-zirgar jama'a da safarar kayayyaki a wannan kasa da ke da mutane miliyan tamanin da biyu, lamarin da ya kawo nakasu ga zirga-zirgar fasinjoji da kayayyaki.