1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaMasar

EgyptAir ya fara zirga-zirga zuwa Sudan

Zainab Mohammed Abubakar
September 5, 2023

Masar ta dawo da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci kai tsaye zuwa Sudan, tun bayan kazamin yakin da ya barke tsakanin hafsoshin sojin kasar watanni biyar da suka gabata.

Masar-Sudan
Masar ta fara zirga-zirga a SudanHoto: picture-alliance/Zuma Press/P. Andrieu

Jirgin kamfanin EgyptAir na Masar na farko, ya taso daga Alkahira, babban birnin kasar da sanyin safiyar wannan Talata zuwa birnin Port Sudan a gabashin Sudan da ke gabar tekun Bahar Maliya, dauke da fasinjoji 120.

Mahukuntan Sudan sun yi maraba da jirgin na Masar ta hanyar watsa masa ruwa na karramawa bayan saukarsa. Sameh Farouq da ke zama karamin jakadan kasar Masar a birnin ya halarci bikin saukar jirgin na farko. A hanyarsa ta dawowa, jirgin ya dauko fasinjoji 115 zuwa birnin Alkahira da yammacin yau din, in ji EgyptAir.

Kamfanin jiragen sama na Egypt Air zai ci-gaba da jigilar fasinja na mako-mako zuwa Port Sudan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na MENA na kasar Masar ya bayyana.