Saudiyya ta katse jiragenta zuwa Kanada
August 7, 2018Talla
Rikicin dipolomasiyya da ke tsakanin masarautar Saudiyya da kasar Kanada, na ci gaba da ruruwa, inda a baya-bayannan kamfanin jiragen saman Saudiyyan ya sanar da dakatar zirga-zirgar dukkannin jiragenta zuwa Toronto.
Makasudin daukar wadannan matakan dai, shi ne suka da Kanada ta yi kan sabon yunkurin kama mata da 'yan gwagwarmayar kare hakkin dan Adam a Saudiyya. Abin da Saudiyyar ta kira "shisshigi da neman wuce makadi da rawa" a harkokin cikin gida.