1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiragen Tornado sun isa Afganistan

April 5, 2007

Jiragen sama na sintiri na jamus guda shida ,da zasu taimakawa dakarun kungfiyar tsaro na NATO dake Afganistan sun isa sansaninsu dake Mazar-e-Sharif.A ranar litinin ne kuma ake saran cewa,Jiragen kirar saukan ungulu mallakar kamfanin Tornado ,zasu fara aiki a karkashin dakarun na NATO,inda zasu fara gudanar da ayyukan sintirin sararin samaniya a kudancin Afganistan a ranar 15 ga watan Afrilu.Wadannan jiragen dai zasu taimaka ne wajen samarda bayanai wa dakarun sojin kasa dake yakar sauran burbudin mayakan Taliban a wannan yankin.A watan daya gabata nedai yan majalisar dokokin Jamus suka amince da tura jiragen,hade da jamian soji 200.