1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta koma barin wuta zirin Gaza

Mahmud Yaya Azare SB
June 16, 2021

 Isra'ila ta sanar da cewa jiragen yakinta sun kai  hare-haren da ta kira na ramuwa kan zirin Gaza na Falasdinu, bayan da wasu bala-balan da aka tura daga zirin na Gaza suka jawo tashin gobara a yankunan Isra'ila.

Erneute Angriffe in Gaza City
Hoto: Mahmud Hams/AFP

Hamas dai ta tabbatar da cilla gomman balan-balan zuwa cikin  Isra'ila a ranar Talata, don mayar da martini da tattakin da Yahudawa masu ra'ayin nuna kyama ga Larabawa suka gudanar, don nuna murna da mamaye birnin Kudus da Isra'ila ta yi a shekarar 1967. Hukumar kashe gobara ta Isra'ila dai ta tabbatar da cewa, bala-balan na Hamas sun jawo barkewar gobara a yankuna kimanin 20 a kudancin Isra'ila. Sai dai ba a tabbatar ko akwai wadanda  suka  jikkata ba.

Karin Bayani: Rikicin Israila da Gaza an kasa tsagaita wuta

Hoto: Tsafrir Abayov/AP/picture alliance

Wannan ne rikicin farko tsakanin Isra'ila da Hamas tun da a ka tsagaita wuta ran 21 ga watan Mayu. Dama dai kungiyar Hamas a baya tasha alwashin maid a mumunan martini dama yiwuar yaki ya dawo ruwa tsakaninta da Isra'ila sakamakon wannan tattakin da ada Yahudawan suka saba gudanar dashi cikin yanayin neman takala da tsokana,amma a wannan karon, duk da cewa sabuwar gwamnatin firaminista Naftali Bennett ta bai wa Yahudawan 'yancin shiga duk yadda suka ga dama, jami'an tsaron Isra'ila da adadinsu ya ninka masu tattakin ninkin ba ninki, sun yi wa tattakin linzami, don kauce wa yin fito na fito da dubban Falalsdinawa da suka ja daga a farfajiyar masallacin na Al-aqsa da ma unguwannin da ke kusa da shi, lamarin da ya jawo jami'an na Isra'ila suka kame Falalsdinawa masu yawa 'yan ta-kife.

Wani kakakin kungiyar Hamas, Mustafa Diyaudden , yace har yanzu a shirye suke da gwabza yaki da Isra,ilan muddin za ta ci gaba da keta hurumin wurare masu tsarki da alfarma na Musulmai.

Kadan dai ana iya tunawa, kutsen da Yahudawa masu ra'ayin rikau suka yi cikin masallacin Al-aqsa mai alfarma a ranakun goman karshen azumin Ramadanan da ya gabata, shi ya jawo barkewar dauki ba dadi na kwanaki 11 tsakanin kungiyoyin gwagwarmaya na Falalsdinawa da Isra'ila.