1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Jiragen yakin Isra'ila sun yi barin wuta a Yemen

Abdoulaye Mamane Amadou
July 20, 2024

Dakarun tsaron Isra'ila sun yi barin wuta kan mabuyar mayakan Houthi da ke Yemen a wani mataki na martani kan harin jirage da kungiyar ta kai a birnin Tel-Aviv na Isra'ila.

Hoto: Nir Elias/Pool Photo/AP/picture alliance

Isra'ila ta sanar da cewa jiragen yakinta sun yi ruwan wuta kan muhimman wuraren da mayakan Houthi ke rike da su a yankin Hodeida da ke yammcin kasar Yemen, a wani abin da Isra'ilar ta kira martani kan hare-haren jirage marasa matuka da kungiyar ta yi ikirarin kaiwa a birnin Tel-Aviv tare da kashe mutum guda.

Karin bayaniHarin Tel Aviv ya kashe mutum guda da raunata wasu 10

A wata sanarwar da ya fitar jim kadan bayan harin na Isra'ila, kakakin kungiyar Houthi Mohammed Al-Bukhaiti, ya bayyana cewa Isra'ila za ta dandana kudarta bayan ta kai harin.

Karin bayani : Hamas ta dakatar da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

Kungiyar Houthi ta shiga fada ne gadan-gadan da Isra'ila, tun bayan da ta kaddamar farmaki a yankin Falasdinu a samamen da ta ce tana kai wa kungiyar Hamas da ke Zirin Gaza.