1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiragen yakin Kenya sun kai hari a kudancin Somaliya

January 17, 2012

Wata kungiyar 'yan tawaye a Somaliya ta yi zargin cewa jiragen yakin Kenya sun kai harin da ya kai ga hallaka wasu kananan yara biyar wadanda basu ji basu gani ba

**FILE** In a Tuesday Nov. 4, 2008 file photo, Somali militia of Al-Shabab are seen during exercises at their military training camp outside Mogadishu. Islamic fighters now control most of southern and central Somalia, with the crucial exceptions of Mogadishu and Baidoa. Islamic fighters declared Thursday, Nov. 13, 2008, that they will use strict Muslim rules to bring their lawless Horn of Africa country back under control. (AP Photo, File)
Dakarun Al-ShababHoto: AP

A Somaliya, wani mai magana a madadin wata kungiyar masu tada kayar baya, da mazauna wani yanki a kudancin kasar, ya ce jiragen yakin Kenya biyu sun kai harin da ya hallaka wadansu kananan yara guda biyar a maimakon wani sansanin sojin yankin da suka yi niyyar tarwatsawa. Ko da shi ke kakakin rundunan sojin Kenyan ya ce jiragen sun kai hari ne kan wani sansanin 'ya'yan kungiyar al-shabab. Wadannan zarge-zarge sun biyo bayan watannin da aka shafe ana ba hammata iska tsakanin dakarun Kenya da 'yan kungiyar al-shabab. Bangarorin biyu suna amfani da shafukan sada zumunta na yanar gizo wajen yada manufofinsu, suna kuma dora laifi kan juna, amma babu 'yan jaridan da suka tantance sahihancin bayanan da ke kan shafukan. Mr Charles Owino shine mataimakin shugaban 'yan sandan Kenya ga kuma abun da ya bayyana dangane da wannan batun:

" Gwamnatin Kenya bata da niyya kai hari kan fararen hula kuma shi ya sa ta kan yi taka tsantsan wajen kai harin, to amma wata sa'a magabta sukan yi amfani da fararen hulan su yi garkuwa, shi ya sa a wasu lokuta harin kan shafi wadanda basu ji ba su gani ba"

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi