Jirgi a Pakistan ya yi hadari da mutane 47
December 7, 2016Talla
Wani jirgin sama mallakar kasar Pakistan dauke da fasinja 47 ya yi hadari a ranar Laraban nan yayin da yake kan hanyarsa tsakanin birnin Chitral na Arewacin kasar zuwa Islamabad kamar yadda mahukuntan da ke lura da harkokin sufurin jiragen sama suka bayyana a kasar.
Masu aikin agaji dai sun bayyana cewa kawowa yanzu mutane 36 ne suka rasu ana kuma sa ran adadin zai karu. Karamin jirgin dai mai suna ATR-42 ya fadi ne a garin Hawalian a Arewacin Pakistan, garin da ked a tazarar kilomita 75daga Areawacin babban birnin kasar ta Pakistan.