Jirgin Boeing Dreamliner ya koma aiki
April 27, 2013Karon farko,bayan watani uku, a wannan Asabar kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Ethiopian Airlines, ya jaraba tashin jirgin Dreamliner, mallakar kamfanin Boeing na kasar Amirka.
Ranar 16 ga watan Janairun shekara bana, Hukumar dake kula da zirga-zirga jiragen sama ta Amirka, ta hana tashin jirage samfarin Dreamliner, dalili da matsalar zafin batur da aka gano.
A duk Afirka kasar Ethiopiya kadai ta mallaki wannan jirgi na zamani.
Kamafanin Ethiopian Airlines ta jaraba daya daga jiragen Dreamliner uku da ya mallaka, wanda ya tashi daga birnin Adis Ababa zuwa Nairobin kasar Kenya.
Shima kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Japan, wato All Nippon Airways zai jaraba tashin Dreamliner ranar Lahadi.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman