1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin jirgin ruwa ya kashe mutane 24 a Najeriya

Abdourahamane Hassane
September 11, 2023

Akalla mutane 24 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka bace a nutsewar wani jirgin ruwa dauke da manoma a kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu a tsakiyar Najeriya kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta sanar.

Hoto: Emmanuel Osodi/UIG/IMAGO

Jirgin kwale-kwale na dauke da manoma sama da dari da ke tsallaka kogin Neja domin zuwa gonakinsu ta wani bangaren, a jihar Neja. yayin da jirgin ya kife. Garba Salihu,shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar.ya ce a halin yanzu, an gano gawarwaki 24 sannan an ceto mutane 30. Nutsewar jiragen ruwa akan kogunaa Najeriya  na faruwa ne saboda yawan lodin jiragen dake yin oba,  da rashin kulawarsu ko rashin bin ƙa'idodjin da suka dace.