1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin Lufthansa ya yi saukar gaggawa a Masar

March 6, 2026

Da farko an tsara jirgin zai tafi Saudiyya ne amma daga bisani aka karkatar da shi zuwa Alkahiran Masar saboda tsaro.

Jirgin Lufthansa yayin da ya ke sauka
Jirgin Lufthansa yayin da ya ke saukaHoto: Hannes P. Albert/dpa/picture alliance

Wani jirgin saman Lufthansa da ya tashi daga birnin Munich na Jamus zuwa Riyadh na Saudiyya ya yi saukar gaggawa a birnin Alkahiran Masar a yau Juma'a saboda dalilai na tsaro sakamakon rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

Babban jami'in kamfanin Lufthansa, Carsten Spohr, ya ce matuƙin jirgin ne ya yanke shawarar karkatar da shi zuwa Alkahira bayan ya tattauna da hedikwatar kamfanin da ke Frankfurt.

Barazanar yajin aiki a kamfanin jiragen saman Lufthansa

Ya ce, “tsaro shi ne abu na farko muhimmi da ya kamata a mayar wa hankali musamman a irin wannan lokacin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya."

A cewar Lufthansa, filin jirgin saman babban birnin Saudiyya, wato Riyadh, ya kasance a rufe a lokacin da jirgin ke shirin sauka.

Kamfanin jiragen sama na Lufthansa zai rage ma'aikata 4,000

Kamfanin ya ce har yanzu jirgin na Lufthansa da zai taso daga Saudiyya wanda tuni ya cika da fasinjoji  bai taso ba tukunna

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW