Jirgin ruwa ya kama da wuta a tsakiyar kogi a Najeriya
August 8, 2024Talla
Jirgin ruwan ya tashi daga garin Ekene da misalin karfe 3 na yammacin wannan Alhamis don zuwa birnin Yenagoa, babban birnin jihar. Rahotanni sun ce kimanin mutum 20 da ke cikin jirgin ruwan sun kone kurmus, yayin da aka ce wasu daga cikin fasinjojin jirgin sun nutse cikin ruwa a kokarinsu na kauce wa gobarar da ta tashi a jirgin.
''Jirgin ruwa ne na 'yan kasuwa da ke dauke da tataccen man fetur ya kama da wuta. Babu gamsassun bayanai kan wutar da ta kama a jirgin.'' in ji Mr Morris Alagowa, jami'i a kungiyar kare muhalli ta Environmental Rights Action, Friends Of The Earth
Kawo yanzu rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa ba ta kai ga fitar da wata sanarwa kan wannan hatsariba.