Jirgin sama mai saukar ungula na sojojin Masar ya fadi
January 25, 2014Wani jirgin sama mai saukan ungulu mallakin sojin kasar Masar ya yi hadari, inda ya hallaka sojoji biyar. Tuni rundunar sojin kasar ta tabbatar da faruwar lamarin na wannan Asabar a yankin Sinai.
A wani labarin jami'an kasar sun yi harbi cikin iska, domin tarwatsa masu zanga-zangar nuna kiyayya ga gwamnatin kasar da ke samun tallafin sojoji. A wannan Asabar aka cika shekaru uku da fara juyin-juya halin da ya kawo karshen gwamnatin Hosni Mubarak ta kasar Masar a sheara ta 2011.
Boren jama'a ya kai ga kifar da gwamnati ta Mubarak da ta kwashe shekaru 30 kan madafun iko. Amma tun daga lokacin kasar ta fada radanin siyasa.
An jibge dafifin jami'an tsaro musamman a Alkahira babban birnin kasar, domin kare yuwuwwar samun tashin hankali daga magoya bayan zababbiyar gwamnatin Mohamed Mursi da aka kifar cikin shekarar da ta gabata. Akwai tsoro a zukatan mutane ganin hare-haren da aka kai a wannan Jumma'a da ta gabata. Fiye da mutane dubu sun hallaka tun bayan juyin mulkin na shekarar da ta gabata.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba