Jirgin sama na Bangladesh ya yi hadari
March 12, 2018Talla
Jirgin wanda ke dauke da fasinja 71 wanda ya taso daga birnin Dacca ya fadi kafin ya isa a filin saukar jiragen sama na Kathmandu. Wani wanda ya shaida lamarin ya ce ya ga lokacin da jirgin ya fadi, ya ce farko sun ga hayaki ya turnike sama kafin da baya su ji wani kara.