1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin sama ya kama da wuta bayan hadari a Tokyo na Japan

Mouhamadou Awal Balarabe
January 2, 2024

An kwashe daruruwan fasinjoji, amma ana neman mutane biyar da suka bace a jirgin kirar Airbus da ya taho daga Sapporo da ke yankin arewacin Japan. Kawo yanzu babu bayani game da musabbabin hadarin.

Jirgin Japan da ya yi hadari a filin tashin jiragen sama na Haneda da birnin Tokyo
Jirgin Japan da ya yi hadari a filin tashin jiragen sama na Haneda da birnin TokyoHoto: Issei Kato/REUTERS

Wani jirgin sama mallakin kasar Japan ya kama da wuta a filin jirgin saman Tokyo-Haneda, inda wasu kafafen yada labarai ke nuna yiwuwar karo da wani jirgin na daban. Tashar talabijin ta NHK mallakin gwamnati ta ruwaito cewar an kwashe akasarin daruruwan fasinjojin da ke cikin jirgin saman, amma ana ci gaba da neman mutane biyar da suka bace. Wannan jirgin kirar Airbus ya taho ne daga Sapporo da ke yankin arewacin Japan a lokacin da ya bugi wani jirgin mallakin masu gadin gabar tekun Japan. Amma kawo yanzu babu bayani game da musabbabin hadarin.

Karin bayani: Sama da bakin haure 60 sun sake mutuwa a hadarin jirgin ruwa

Ba a dai cika samun hatsarin jiragen sama a kasar Japan ba. Sai dai hadari mafi muni ya faru ne a shekarar 1985, inda ya kashe mutane 520. Wannan hadarin ya zo ne kwana guda bayan ibtila'i na girgizar kasa da ya afku a yankin Noto da ke tsakiyar kasar Japam, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 48.

     

2024-01-02T10:43:26Z UTC