Jirgin saman Rasha ya fadi da mutane 224
October 31, 2015Jirgin sama mallakin kamafnin kasar Rasha ya fadi a cikin yankin Sinai na kasar Masar, kuma rahotannin da hukumomin kasar ta Masar na cewa an gano akwatin nadan magana na jirgin. Jirgin sama ya yi hadari dauke da mutane 224.
Tuni Shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha ya ba da umurnin tura tawogar taimako zuwa Masar domin gano aikin ceto. Shugaban ya kuma ayyana gobe Lahadi daya ga watan Nowamba a matsayin ranar zaman makoki bisa abin da ya faru. Mahukuntan Masar sun ce daukacin fasinjojin da ke cikin 'yan kasar Rasha ne. Sannan sun nuna cewa akwai mutane da dama da suka mutu sakamakon hadarin.
Wannan jirgin sama da ya yi hadari ya taso daga birnin yawon bude na Sharm el-Sheikh da ke kasar Masar a kan hanyar zuwa birnin St. Petersburg na kasar Rasha.