1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Joe Biden ya soma ziyarar farko da taron G7

Ramatu Garba Baba
June 9, 2021

Shugaban Amirka Joe Biden ya soma ziyararsa ta farko da zai yi a wata kasa tun bayan dare mulki da halatar taron G7 na kasashen duniya masu karfin tattalin arziki.

USA | Tulsa | Gedenken an Greenwood Massaker 1921
Hoto: Evan Vucci/AP/dpa/picture alliance

Shugaba Joe Biden na Amirka ya kama hanyar zuwa taron kasashen duniya na masu karfin tattalin arziki na G7 da za a soma a Britaniya a wannan makon, ziyarar ce ta farko da Biden ke yi a wata kasa, tun bayan dare madafun iko a farkon wannan shekarar ta 2021.

Baya ga taron na G7, shugaban mai shekaru 78 da haihuwa, zai wuce birnin Brussels na kasar Belgium domin halartar taron Kungiyar tsaro ta NATO dana Kungiyar tarayyar Turai, kafin ya karkare ziyarar tasa da wata ganawa da aka tsara a tsakaninsa da Shugaban Rasha Vladimir Putin a ranar Laraba mai zuwa.

Ana ganin, Biden na son amfani da wannan dama a maido dama farfado da dangatakar kasar da kasashen duniya, da ta tabarbare a sakamakon gangancin da katobara da ake zargin tsohuwar gwamnatin Donald Trump da yi.