John Kerry na shirin zuwa Najeriya kan Boko Haram
January 23, 2015Talla
Kerry ya sanar da aniyar ce a yau Jumma'a, cikin wani jawabi da ya yi kan harkokin ta'addanci a babban taron kasashen duniya kan tattalin arziki da ke gudana a birnin Davos na kasar Switzerland. John Kerry ya yi jan hankali na ganin cewa kada a karkata akalar ya zuwa kyamar Yahudawa ko kuma kyamar mabiya addinin Islama, a yakin da ake yi da 'yan kungiyar IS, da Al-Qaida ko kuma Boko Haram.
Kasar ta Najeriya dai na cikin shirye-shiryen zaben shugaban kasa da 'yan majalisun Tarayya da za su gudana a ranar 14 ga wata Febrairu mai zuwa, inda a wannan Jumma'ar hukumar zaben kasar ta tabbatar cewa, ba za a daga zabe ba kamar yadda wasu ke neman ayi
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman