John Kerry na ziyara a kasar Masar
June 22, 2014Yayin wannan ziyara, John Kerry ya tattauna batun makomar 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi, da kuma rikicin kasar Iraki, ta yadda yake wata babbar barazana ga kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya baki daya.
Wannan dai ita ce ziyarar wani babban jami'in kasar Amirka ta farko a wannan kasa, tun bayan rantsar da Shugaba Al-Sissi, wanda shi ne ya jagorancin kifar da gwamnatin zabeben Shugaban kasar Mohamed Morsi, sannan kuma hukumomin na Masar suka ayyana kungiyar ta 'yan uwa Musulmi ta Mohamed Morsi, a matsayin ta 'yan ta'adda.
Wannan ziyara ta Kerry, ta zo ne a kwana daya, bayan da kotun kasar ta Masar, ta yanke wa shugaban kungiyar ta 'yan uwa Musulmi Mohamed Badie, hukuncin kisa tare da wasu mutane 182 magoya bayan kungiyar.
Kasar ta Amirka dai ta ce a shirye take tayi hulda da sabon shugaban na masar, amma kuma tana da shakku kan batun kare hakkokin Bil-Adama a wannan kasa.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba