John Mahama ya gana da Tinubu kan batun kasashen Sahel
March 29, 2025
Nadin sabo na shugaban kasar Ghana dai na zaman sabon fata na kai wa ya zuwa lallashi da kila ma yin sulhu a tsakanin kasashen ECOWAS da kuma takwarorinsu na Sahel guda Uku. Kuma John Mahama da ya karade kasashen guda uku yana tattaunawa a cikin gwada sa'ar da ke zaman kan-kan da ta zakara, dai ya ce da akwai sarkakiyar da ke da girman gaske cikin rikicin da ke tsakanin ECOWAS da kasashen.
Mahama da ya gana da Tinubu bayan kamalla nasa zagayen dai yace ana bukatar karin tattaunawa a tsakani na bangarorin biyu kann hanyar rabe zare da abawa .‚‘‘Nazo Abuja ne domin in ba shi bayani kan ziyarar da na kai kasashe na kawancen Sahel na Burkina Faso da Niger da kuma Mali.Kuma in shaida musu wasu daga cikin damuwar da na samo daga kasahen guda Uku.
Abu ne dake da sarkakiya mai girma, kuma yana bukatar karin tattaunawa da wadancan kasashen. Domin ganin yadda za mu cigaba da hada kai tare dasu.‘‘‘
A cikin watan Janairun da ya shude ne dai kasashen guda uku suka kai ga ficewa daga ECOWAS bayan share tsawo na lokaci ana lallashi ba tare kwalliya biyan kudi na sabulun wanki ba.
To sai dai kuma majoyoyi sun tabbatar da bude sabuwar tattaunawa a tsakani na bangarorin biyu da ke da damuwa ta tattali na arziki dama tsaro, kuma ke da bukata na tallafin jjunansu.