1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

071011 Johnson-Sirleaf Nobelpreis

October 7, 2011

Shugabar ƙasar Liberiya Ellen Johnson-Sirleaf tare da wasu mata biyu Leyman Gbowee da Tawakkul Karman sun samu kyautar Nobel ta zaman lafiya.

Ellen Johnson-SirleafHoto: picture-alliance/dpa

A cikin watan Nuwamban shekarar 2005 aka zaɓi Ellen Johnson-Sirleaf a mukamin shugabar ƙasar Liberiya, wanda haka ya sa ta zama mace ta farko da ta ɗare kan kujerar shugabancin wata ƙasar Afirka. Johnson-Sirleaf wadda mai shekaru 72 a duniya, ta karɓi jagorancin Liberiya ne bayan yaƙin basasan shekaru 14 da ƙasar ta yi fama da shi, wanda kuma yayi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 250 tare da ɗaiɗaita ƙasar.

A cikin wani gajeren jawabin nuna farin cikinta da samun wannan kyautar, Johnson-Sirleaf cewa ta yi wannan karramawa ce ga al'umar Liberiya.

"Na karɓi wannan kyautar da sunan al'umar Liberiya. Su suka cancanci yabo. Mun samu zaman lafiya a cikin shekaru takwas da suka wuce, kuma ko wane daga cikin su ya ba da gudunmawa wajen wanzuwar zaman lafiyar."

Tuni dai wasu 'yan Liberiya a ciki da wajen ƙasar sun fara tofa albarkacin bakinsu game da kyautar zaman lafiyar da a bana mata biyu a ƙasar wato Johnson-Sirleaf da Leymah Gbowee wata mai fafatuka a Liberiya. Wannan dai shi ne karon farko tun bayan shekarar 2004 da aka ba da kyautar zama lafiya ta Nobel ga matan Afirka. Ethel Davis ita ce jakadiyar Liberiya a Jamus, ta nuna farin cikinta da wannan kyautar.

"Na yi murna. Yau kyakkyawar rana ce ga mutane Liberiya, da matan Liberiya da matan Afirka baki ɗaya. Yau wata ranar murna ce. ta farko ita ce ranar da ta ci zaɓen shugabar ƙasa sannan yau aka ba ta wannan kyauta. Mun yi murna sosai."

Shi ma James Dorbor Jallah tsohon ministan tsare tsare na Liberiya cewa yayi shugabar ta cancanci wannan karramawa musamman saboda aikin da ta yi wa 'yan ƙasar.

"Ta yi wa Liberiya aiki da yawa wanda ya yi kyakkyawan tasiri ga mutane da yawa da nahiyar da duniya baki ɗaya. Har yanzu Afirka wata nahiya ce da maza suka yiwa babakere. Saboda ganin an karrama wata mace daga wani ƙauye dangane da rawar da taje takawa a fagen siyasa, kyakkyawan saƙo ne ga nahiyar baki ɗaya."

Wannan kyautar dai ta zo ne kwanaki huɗu gabanin zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a Liberiya, inda Shugaba Johnson-Sirleaf take neman yin tazarce, ta sa an fara ta da jijiyar wuya a kwanakin ƙarshe na yaƙin neman zaɓe. Masu adawa da ita sun bayyana lokacin sanar da kyautar da cewa tsonkana ce ga zaɓen na ranar Talata mai zuwa. A daidai lokacin da duniya ke kwatanta ta da mace mai kama da Nelson Mandela, Sirleaf na fuskantar ƙalubale daban daban a gida, inda masu sukar lamirinta suka ce ba ta yi wani abin a zo a gani ba.

Sauran waɗanda za su raba kyautar zaman lafiyar da ita su ne Leymah Gbowee 'yar Liberiya kuma shugabar wata ƙungiyar mata farar hula mafi girma a Afirka dake gwagwarmayar wanzar da zaman lafiya da tsaro a Afirka sai kuma Tawakkul Karman 'yar jaridar ƙasar Yemen mai fafatukar girke demokraɗiyya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi