Jonathan ka iya tsayawa takara
May 28, 2010Amirka ta bayyana goyon bayanta na tsayawan shugaban Najeriya a zaɓen da za'a gudanar a shekara mai zuwa muddin hakan bai saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasa ba. Sakatariyar harkokin wajen Amirka mai lura da Demokiraɗiya da harkokin mulki a duniya Maria Otero ta sanar da hakan bayan ta gana da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a fadar shugaban ƙasa dake Abuja. Kafofin yaɗa labarai a fadar shugaban ƙasar sun ruwaito ƙaramar sakatariyar harkokin wajen ta Amirka na cewar, zaɓe na adalci ne kawai zai tabbatar da cigaban Najeriya kuma wannan shine babban ƙalubalen dake gaban shugaba Jonathan. A jiya ne dai aka ruwaito shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan yana baiyana ƙudirin gwamnatin sa na ƙaddamar da kotun musanman da za ta yiwa masu tafƙa maguɗin zaɓe hukunci irin na karta kwana domin zama aya ga 'yan siyasa da kuma jami'an hukumar zaɓe.
Mawallafi: Babangidsa Jibril
Edita: Mohammad Nasiru Awal