1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jonathan ya cika rabin wa'adin mulkinsa

May 29, 2013

shugaban Najeriya ya yaba nasarorin da gwamnatinsa ta cimma a tsukin shekaru biyu da su ka wuce.Ya kuma dauki sabin alkawura a shekaru biyu masu zuwa.

Nigeria Tag der Demokratie (29.05.2013): Nigerias Präsident Goodluck Jonathan; Copyright: DW/U. Musa
Bikin cikar shekaru biyu da fara mulkin Jonathan wanda yayi daidai da ranar Dimokaradiya a NajeriyaHoto: DW/U. Musa

A wani abun da ke zaman kama hanyar zama magori wasa kanka da kanka, gwamantin Tarayyar Najeriya ta ce ta yi rawar gani wajen kawo sauyi ga rayuwar al'umma a tsawon shekaru biyun da ta share a gadon mulki

An sha biki da owambe an kuma ci har an yi hani'an amma kuma duk a cikin mummunan tsaron da ko bayan jami'an tsaron da yawansu ke shirin kankankan da bakin da aka gaiyyata ya hada har da jirgin saman da ke shawagi kan harabar dandalin bikin demokaradiyyar kasar ta Najeriya.

To sai dai kuma duk da haka gwamantin kasar ta ce ta ji ta gani ta kuma kokarta wajen kafa tarihin sake tsara kasar ya zuwa hanyar ci-gaban tattalin arziki da zamantakewa.

Jonathan tare da Namadi SamboHoto: DW/U. Musa

A cikin wani littafin da ya kaddamar mai shafuka kusan 250 dai shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan yace ya gani kuma ya sauya ga batun samar da wutar lantarki da harkokin sufuri da ma batu na ci-gaban tattalin arzikin da ya maida kasar babu kamar ta a nahiyar Afirka baki daya. A cewar shugaban da har ila yau ya soki irin salon auna gwamnatin da kafafen yada labaran kasar ke dauka.

"Dabarar itace ta gabatar ma ku da bayanan aiyukan gwamnatin nan na cikin shekaru biyun da su ka wuce, ga duk 'yan Najeriya domin ba da dama ga masu nazarin harkokin gwamnatin su gina ma'aunin aunata.

Ina rokon duk ma su son rubuta ko sharhi kansa su fidda ma'auni da zai ba su damar kwatanta shekaru biyun da duk wata gwamnati a nahiyar Afirka ba'a Najeriya ka dai ba domin aunin"

Dabarar kuma da tun ba'a kai ko ina ba ta gaza burge 'yan kasar da dama da ko dai suka zabi bacci a cikin gidajensu ko kuma mantawa da ana biki a gidan nasu ga Abujar da titunan ta ke kamar an share kuma babu alamar murnar cika shekaru 14 na demokaradiyyar balle shekaru biyu na gwamnatin Jonathan.

Tuni ma dai 'yan adawar kasar su ka fara kiran karatun coje ga daukacin nasarorin da gwamantin ke ikirarin samu nasarorin kuma da a cewar Injiniya Buba Galadima da ke zaman Sakataren jam'iyyar CPC ta adawa su ka tsaya a cikin tunanin mahukuntan na Abuja.

Siyasa da kokarin ginin kasa ko kuma wasa da hankalin talakawa dai a waje daya,kasar ta Najeriya ta na karatun sabon karni na ci-gaban da ya maidata zuwa 'yan mora a duniya, a gefe kuma al'ummarta na ci-gaban da karatun fatara da rashin tsaron da ya addabi talaka sannan kuma ke barazana har ga sarakunan da ke mulki cikin kasar.

Jam'iyyar ACN mai adawaHoto: DW/U. Musa

To sai dai kuma a tunanin Ali Ahmed Gulak da ke baiwa shugaba Jonathan shawara ga batun siyasa dai adawa ta kai ga toshe zuciyar masu ita ga duk wani kokari na sauyin da kasar ke fuskanta yanzu haka.

Abun jira a gani dai na zaman mafita ga kasar da ta share shekara da shekaru ta na neman sauyi amma kuma ke kara tsunduma a cikin rikici na siyasa da tattalin arzikin al'ummarta.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita:Yahouza Sadissou Madobi