Jonathan ya kaddamar da takararsa a zaben 2015
November 11, 2014A cikin wani bikin da ya samu halartar kwai da kwarkwatar jam'iyyar ta PDP ne dai Shugaba Joantahan ya kai ga amincewa da bukatar da ta dauki hankali ciki da wajen Najeriya. Sanarwar ta jonathan dai ta kai karshen doguwar taci- ba- taci ba da ta mammaye jam'iyyarsa ta PDP da fagen siysaar kasar na lokaci mai nisa. Sai dai kuma akasin shekaru hudun da ya bullo a matsayin mataimakin shugaban kasar da bashi da takalmi a kafa, Goodluck Ebele Jonathan ya sake jefa malafar tasa a filin daga ne tare da shirgin rashin tsaro dama iya mulkin da suke neman kaishi kasa.
Garuruwan da dama arewacin kasar na hannun daular Shekau yanzu haka. sannan kuma ga kari na kwararar jini ta ko'ina cikin ita kanta daular ta Jonathan. Lamrun da bisa ga dukkanin alamu ke dada nuna irin jan aikin dake akwai a tsakanin magoya bayan shugaban kasar dake shirin tallarsa cikin mawuyacin hali.
Ra'ayoyi kan takarar Jonatahan karkashin PDP
Sai dai kuma gwamna Ibrahim Hassan Dan kwambo na Gombe da ya halarci taron daga yankin Arewa maso Gabashi dake dada fuskantar tasku a yanzu, ya ce goya baya ga Jonathan din ne ke zaman hanyarsu ta kaiwa ga tabbatar da kawo karshen matsalar dake kara rage musu dangi yanzu.
'Yan Borno dake zaman cibiyar rikicin tun daga farkon fari dai, su basu ganin gazawa ta shugaban kasa a yakin da ya rusa tattalin arziki na al'ummarsu a cewar Shetima Bulama dake neman tsayawa PDP gwamna a jihar. “ Ai ba shugaban kasa ba ne ya kawo Boko Haram a kasar nan, kuma ba shi ne yake biyan 'yan kungiyar don su ci gaba da kalubalen da suke yi ba. Shi yana son kawo zaman lafiya, kuma abu ne da ya wuce hankali fiye da yadda ake zata”
Jonathan din ya fito takara tare da rudanin ko wa'adinsa na zaman na tazarce ko kuwa har yanzu da damarsa cikin kundin tsarin mulkin kasar ta Najeriya. Alhaji Sule Lamido dai na zaman daya daga cikin wadanda suka kai ga ja da shugaban akan sabawar alkawari, kafin daga baya ya yi juyin 'yar tsala tare da kaiwa ga kasancewa a Abuja don mubaya'a ga shugaban. “ Ban ce ba hayaniya ba tsakaninmu, akwaita. Amma dai hayaniyar gida ba zata ba na waje damar riba ba. Sauran abokan hamaya don lalaci basa komai don neman jama'a sai suyi kwance suna fatan hayaniyar PDP zata kaisu ga nasara. ”
Kasancewar Lamido a cikin manyan jam'iyyar daga yankin Arewa maso yamma na nuna alamar kokarin dinkewar 'yan PDP na wannan yankin, da nufin tunkarar barazana mafi girma ta adawar dake kara girma da tasiri a tsakanin 'yan yankin na Arewa maso Yamma.