1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angola na jimamin mutuwar Dos Santos

Ramatu Garba Baba
July 8, 2022

Tsohon shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos ya mutu a wannan Jumma'ar yana da shekaru 79 a duniya. Ya mutu bayan ya sha fama da jinya a wani asibiti a kasar Spain.

Jose Eduardo dos Santos
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

A wata sanarwar da gwamnatin ta fitar a shafinta na Facebook, ta ce, tsohon shugaban kasar Jose Eduardo dos Santos, ya mutu ne a wani asibiti da ke birnin Barcelona na kasar Spain, bayan da ya sha fama da doguwar jinya. Za a kwashi akalla kwanaki biyar ana zaman makoki bayan da aka sassauta tutar kasar don girmama marigayin bisa umarnin Shugaba Joao Lourenco.

Ana tuna dos Santos da zama adalin shugaba da ya gudanar da shugabancincinsa na kusan shekaru arba'in a lokacin da Angola ta ke cikin hali na rashin tabbas, bayan da ta samu 'yanci kai daga kasar Portugal da ta yi mata mulkin mallaka.