1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Joseph Kony ya aikata mummunar ta'asa

May 21, 2013

Majalisar ƊinKin Duniya ta ce jagoran ƙungiyar yan tawaye ta LRA ,ya kashe sama da mutane dubu ɗari a yankin Afirka ta Tsakiya a cikin shekaru 25 na baya baya nan.

(FILES) A file photo taken on November 12, 2006, shows the leader of the Lord's Resistance Army (LRA), Joseph Kony, answering journalists' questions in Ri-Kwamba, southern Sudan, following a meeting with UN humanitarian chief Jan Egeland. Uganda's rebel Lord's Resistance Army vowed on September 13, 2008 to sign a final peace deal but warned it will not disarm until International Criminal Court arrest warrants for alleged war crimes are 'resolved'. LRA spokesman David Nyekorach-Matsanga said rebel chief Joseph Kony was willing to sign the much delayed peace deal, speaking as military pressure mounts against the northern Ugandan insurgents. AFP PHOTO /STUART PRICE (Photo credit should read STUART PRICE/AFP/Getty Images)
Hoto: Stuart Price/AFP/Getty Images

A cikin wani rahoton da hukumar ta Majalisar Ɗikin Duniyar da ke kare hakin bil addama ta wallafa tun a shekarun 1997 wanda za ta bayyana a nan gaba.

Ta ce haka gugun mayaƙan da Kony ke yiwa jagora ana tuhumar su da laifin sace yara ƙanana kimanin dubu 60 zuwa dubu 100. Waɗanda su suke sakawa cikin aikin soji, duk da ma cewar shekarun su, ba su kai ba. Tare da tilatawa wasu mutane miliyan biyu da rabi barin gidajensu.

Ƙungiyar dai ta LRA wace ke ɗaya daga cikin ƙungiyoyijn da ke yin yaƙin sari ka noƙe tun a shekarun 1988 a yankin arewacin ƙasar Yuganda. Yanzu haka mayaƙanta sun bazu zuwa a yanki arewa maso gabshin Kwango da Afirka ta Tasakiya da kuma Sudan ta Kudu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW