JTF ta ce ta kashe 'yan bindiga a Kano
March 31, 2013Talla
Rundunar tsaro ta hadin guywa a jihar kano wato JTF ta bayyana cewa ta yi nasarar harbe wasu 'yan bindiga 14 yayin wata arangama da safiyar wannan lahadin.Karar harbin bindigogi da fashewar bama bamai sun yi ta tashi a yankin unguwa uku da kanon.
Kakakin rundunar na jihar kano Keptain Ikedechi Iweaha ya bayyana cewar dakarun sun yi artabu da wasu mutane da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram. Ya kuma tabbatar da cewar soja guda ya rasa ransa yayin da wani guda kuma ya sami mummunan rauni . Keptain Iweaha ya kuma nunar da cewa dakarun rundunar sun hallaka 'yan bindiga 14 bayan tarin makamai da bama bamai da suka samu a wasu gidajen.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mouhamadou Auwal Balarabe