Jundullah ta dauki alkahin harin Karachi
May 13, 2015Kimanin mutane 43 sun rigamu gidan gaskiya a birnin Karachi na Pakistan a wani harin da 'yan bindiga suka kai a kan wani bas da ke dauke da tsirarun 'yan shi'an kasar. Tuni dai kungiyar Jundullah da ke da kaifin kishin Islama ta dauki alhakin wannan harin, da ke zama mafi muni a watanni hudu na baya-bayanan.
Wani babban jami'in 'yan sandan Pakistan ya ce 'yan bindiga shida da ke kan babura ne suka yi luguden wuta a kan direba da kuma mutane 60 da ke cikin motar da ya ke tukawa. Tuni dai hapsan hapsoshin sojojin kasar ta Pakistan Janar Raheel Sharif ya soke ziyarar aiki a Sri Lanka sakamakon wannan aika-aika.
Hare-haren na neman zama ruwan dare a birnin Karachi sakamakon haihawar ayyukan ta'addanci a Pakistan. A watan Disemban bara ma dai mutane 154 ne suka sheka lahira a Peshawar a lokacin da 'yan Taliban suka kutswa wata makaranta tare da bude wuta irin na kan mai uwa da wabi.