Justin Trudeau ya lashe zaben Kanada
September 21, 2021Talla
Dan takara na jam'iyyar Conservative mai adawa a Kanada Erin O'Toole, ya amince da shan kaye a babban zaben da suka fafata da firaiminista mai ci, ya amsa shan kayin ne, bayan da alamu suka soma nuna cewa, Firaiminista Justin Trudeau ya sha gabansa a kiddidigar da hukumar zaben kasar ta soma fitarwa tun daga daren jiya Litinin.
Wannan nasara dai, ta bai wa Firaiminista Trudeau wa'adin mulki na uku, a jawabinsa na farko bayan yin nasara, bayan gode ma 'yan kasar da suka sake zabansa, ya ce, wannan wata dama ce, da ya samu domin ya sake farfado da kasar daga ta'asar annobar corona, duk da wannan nasarar, jam'iyyar Liberals ta Firaiministan mai shekaru 49 da haihuwan ba ta kai ga samun rinjaye na kujeru 170 a majalisar kasar ba.