1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Salon juyin mulki a nahiyar Afirka

Usman Shehu Usman SB/MAB
September 22, 2023

Juyin mulkin da aka samu a wasu kasashe rainon Faransa na Agirka ya dauki hankalin jaridun Jamus da ambaliyar ruwa a Libiya.

Goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar NijarHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

Jaridar die WELT wace ta duba mulkin mallakar Turawan Faransa a Afirka. Jaridar ta ce Faransa na jagorantar yaki a sama da shekaru 50. Ta ci gaba da cewa siyasar kasashen tsakiya da na yammacin Afirka ya ci aba da samun na juyin mulki vayan jujen mulki daya vayan daya. Duk gwamnatocin da ake kifarwa ya faru ne a kasashe rainon Fransa. Jaridar ta ce masana sun fara bayyana kura-kuren da Frans ata yi, Wanda kuma ya kamata kasashe kamar Jamus su dau darasi. Juyin mulkin baya-bayan nan shi ne a Gabon. Jaridar ta ce juyin mulkin kasar Gabon ya faru ne dai-dai lokacin da Fransa ke kokari sasantawa da gwamnatin sojan Nijar kan yadda Faransawa za su kwashe sojojinsu daga Nijar. Wanda kuma ya biyo vayan da Faransar aka tilasta mata kwashe sojojinta a kasashen, Mali da Burkina Faso.

Karin Bayani: Jaridun Jamus: Ko sauro ya daina yada cuta?

Tutocin kasashen Faransa da GabonHoto: Aleks Taurus/Pond5 Images/imago images

Ita kuwa Jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi babbar bukata dai Faransa ta fice kawai. Jaridar ta ci gaba da cewa ana son rayu ba tare da faransa. Jaridar ta ci gaba da cewa kai a takaice dai an koshi da batun Faransa a a kasashen da ta yi wa mulkin mallaka. Wannan kuwa bawai kawai wani bangaren tsarin Faransa ne ba a so ba, amma kwai daukacin gwamnati ce ake so wace ba ta dasawa da Faransa. Jaridar ta ce misali a kasar Senegal ba a yi juyin mulki ba, amma kuma akasarin talakawa da yi magana da su suna nuna farin ciki da jinjinawa kan juyin mulki a wasu kasashe makobta. Inda mutanen Senegal ke tan una irin barnar da sojojin mulkin mallaka suka yiwa kasar, musamman kasar Faransa.

Ambaliyar ruwa a Derna da ke kasra LibiyaHoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Frankfurter Allgemeine Zeitungta duba ibtala'in kasar Libiya ne wace balain ambaliyar ruwa ya yiwa mumman barna. Jaridar ta ce amma har yanzu tashin hankali a Libiya na nan, domin maimakon sun hada kaai su taimaki juna, yan kasar ta Libiya da ke rarrabuwar kawuna sai dai kowa ya hadu ya yaba gwaninsa. Wani abun kaito shi ne yadda mako guda kacal da bala'in da ya fadawa Libiya, sai aka yan kasar musamman a gabar ruwan da aka yi ambaliya, jama'a sun fito zanga-zangar kyamar gwamnati suna neman sai a rusa majalisar dokoki da dai sauransu. Yayind a shugabannin siyasa na bangarorin masu gaba da juuna ke cewa suna iya kokarinsu don ceto da kuma tallafawa jama'a, amma akasarin Libiyawa da aka yi magana da su na cewa babu wani dauki da suke samu a bangaren Janar Khalifa Haftar, ko kuma gwamnatin yammacin, duk ko wannensu kujerarsa kawai yake karewa duk da bala'in da kasar ta samu kanta.

Moroko bayan girgizar kasaHoto: Emilie Madi/REUTERS

Sai dai a kasar Moroko da ba rikici ma batun raba kayan agaji ya kai ga nuna rashin jituwa. Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce a yayin da kungiyoyin duniya ke kokarin taimakawa Moroko bisa ga duk alamu aikin samun cikas a kokarin da mahukunta ke cewa kamata ya yi a tabbatar da rarrabawa kayan bisa tsarin raba dai-dai dai. Wannan mataki ya jawo tsaiko da jinmkiri wajen isar da gajin gaggawa ga mabukata. Ga misali wasu daga cikin jami'an bada agajin gaggawa da suka fito daga kasar Spain haka suka koma gida ba tare da yin wani abu ba, saboda kafin su isa yankunan da za su yi aikin kusan ba wanda ke da rai sai dai tarin gawaki. An dai yi kiyasin mutane kimanin 2900 suka mutu wasu sama da 6000 suka jikkata sakamakon girgizar kasa da aka yi.