1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Juyin mulki a Afrika gazawar dimukuradiyya

September 22, 2023

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Guinea Kanal Mamady Doumbouya ya bayyana annobar juye-juyen mulki a kasashen Afrika a matsayin gazawar tasirin dimukuradiyya da kasashen suka gada daga kasashen Yamma.

Shugaban Gine ya tsage garkiya a game da juye-juyen mulkiHoto: BRENDAN MCDERMID/REUTERS

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 wanda ke gudana a birnin New York na kasar Amurka, inda ya ce Afrika na fama ne da salon mulki da aka tilasta mata yi amma kuma wanda bai dace da tsarin al'adun nahiyar ba.

Karin bayani: Juyin mulki na dab da zama yayi a Afirka

Kanal Mamady Doumbouya ya kuma kara da cewa wannan salon mulki ya ba wa wasu kasashe damar wawushe arzikin kasashen Afrika tare kuma da karfafa ci hanci da rashawa a tsakanin shugabannin kasashen nahiyar.

Karin bayani: Kalubalen aikin hakar uranium a Nijar

Shugaban ya karkare yana mai cewa lokaci ya yi da za a yi la'akari da hakkokin kasashen Afrika, a kuma ba wa nahiyar matsayinta, kana kuma a daina yin wasan yara da al'ummomin Afrika a wannan lokaci da kan mage ya waye. 

Karin bayani: Tasirin juyin mulkin Nijar a jaridun Jamus