1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kabila ya sha alwashin shiga tsakani a rikicin Kwango da M23

April 9, 2025

Tsohon shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango Joseph Kabila na ci gaba tattaunawa da 'yan adawa da 'yan siyasa da kungiyoyin fararen hula har ma da wakilan 'yan tawayen M23 wajen warware rikicin DRC.

Hoto: Alain Uaykani/Xinhua News Agency/picture alliance

Tsohon shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango Joseph Kabila ya bayyana cewa a shirye yake wajen dawowa kasar domin shiga tsakani wajen warware rikicin da ke tsakanin DRC da 'yan tawayen M23 da ke samun goyón bayan Ruwanda.

Karin bayani: Mahukuntan DRC da 'yan tawayen M23 za su hau teburin tattaunawa

Kabila ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa lokaci ya yi da ya kamata a warware takaddamar da ke tsakanin Kwango da M23 a kasar dake da arzikin ma'adinai.