1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaboré ya ziyarci soja a fagen daga

Abdoulaye Mamane Amadou
June 19, 2020

Shugaba Roch Marc Christian Kaboré na Burkina Faso ya kai wata ziyarar ba zata don ganewa idonsa halin da dakarun tsaron kasar suke ciki a Djibo da ke arewacin kasar mai fama da hare-haren 'yan masu da'awar jihadi.

Präsident von Burkina Faso: Roch Marc Christian Kaboré
Hoto: DW/M. Schetter

A wani sakonsa na shafin Twitter shugaba Roch Marc Christian Kaboré  ya sha alwashin ci gaba da dorewar tsaro a yankin mai tazarar kilo mita 200 daga arewacin babban birnin kasar Ouagadougou, tare da cewa yankin zai ci gaba da kasancewa karkashin ikon gwamnati duk da barazanar da 'yan ta'adda ta ganin sun dagula al'amura.

Ya zuwa yanzu dai al'ummomin kananan hukumomin yankin tare ne aka ce sun kauracewa gidajensu sakamakon matsin lambar mayakan jihadi da ke kai hari babu kakkautawa.