1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso: Kabore ya lashe zaben shugaban kasa

Ramatu Garba Baba
November 26, 2020

Roch Marc Christian Kabore zai yi wa'adin mulki na biyu bayan da yayi nasarar lashe babban zaben kasar da gagarumin rinjaye. Ya lashe kimanin kashi 57.87 cikin dari na kuri'un da aka kada acewar hukumar zaben kasar.

Burkina Faso Wahl in Ouagadougou Präsdentschaftskandidat Roch Marc Kabore
Hoto: Reuters/J. Penney

Lashe zaben da Roch Marc Christian Kabore yayi da gagarumin rinjaye na nufin ba sai a je zagaye na biyu ba, a sakamakon hakan zai ci gaba da mulki a wa'adi na biyu. Hukumar zaben kasar ta CENI, da ta baiyana sakamakon zaben, ta ce, Kabore ya lashe kashi 57.87 cikin dari na kuri'un da aka kada.Kabore yayi wa sauran 'yan takara fintinkau a zaben da aka gudanar cikin yanayi na fargabar tsaro a ranar Lahadin da ta gabata. Eddie Komboigo ne ya zo na biyu da kashi 15.48 sai kuma Zephirin Diabre wanda bangaren adawa suka marawa baya da ya zo na uku da kashi 12.46 cikin dari na kuri'un. 


Tun kafin baiyana sakamakon zaben ma dai, 'yan adawa sun yi zargin an tafka magudi da wasu kura-kurai daga bangaren hukumar zabe inda suka nuna rashin amince a game da sahihancin zaben kansa. Matsalar tsaro da kasar da ke a yankin Sahel ke fama, yasa jama'a da dama ba su fita don kada kuri'unsu ba. Kabore mai shekaru sittin da uku yana fuskantar suka daga 'yan kasa, kan yada ya gagara shawo kan matsalar masu tayar da kayar baya da ta hana kasar zaman lafiya.