1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kace nace tsakanin tarayyar Turai da Brazil

Mohammad Nasiru AwalDecember 3, 2005

Tarayyar Turai ta ce ba´a gode mata ba duk da rangwamen da ta yi a kungiyar ciniki ta duniya WTO.

Peter Mandelson
Peter MandelsonHoto: AP

Ba wanda zai iya fahimtar halin tsaka mai wuya da kungiyar tarayyar Turai ke ciki a yanzu. Bayan ta mika kai ta bude kofofin kasuwanninta amma duk da haka ana dora mata laifi a dangane da cijewar shawarwarin kungiyar cinikaiya ta duniya. Ga dai abin da kwamishinan cinikaiya na EU Peter Mandelson ke fadi.

“Mun yi tayin rage kudaden tallafi na cinikaiya da misalin kashi 70 cikin 100. Duk da cewa ba shakka dangane da da canje-canjen muka aiwatar, amma har yanzu ba wanda ya yaba mana a tsakanin abokan shawarwarinmu.”

Wannan korafi da Mandelson ya yi tamkar hannunka mai sanda ne ga kasashen kungiyar G-20 musamman kasar Brazil dake magana da yawun wannan kungiya. An shafe shekaru masu yawa ana kai ruwa rana tsakanin Brazil da kungiyar EU a fannin aikin noma. Bayan karar da ta kai a gaban kungiyar WTO, Brazil ta samu nasarar tilastawa EU aiwatar da canje-canje wajen samar da sukari. Amma yanzu kuma Brazil din ce ke zargin EU da rashin bude kofofin kasuwanninta yadda ya kamata ga naman shanu daga Brazil.

Tayin da EU ta yi a fannin aikin noma ga taron ministocin kungiyar WTO a Hongkong ya kasu gida 3. Na farko EU zata soke dukkan tallafin da take ba kayan da take sayarwa ketare. Na biyu zata rage tallafin cinikaiya da kashi 70 cikin 100. Na uku zata rage talafin kayan amfani gona da kashi 60 cikin 100. Yayin da kudin kwastan da zata rage bai shafi wasu kayakin kamar naman shanu ba wanda kasashen kudancin Amirka ke ganin zasu fi yin cinikinsa a Turai. EU ta dauki wannan mataki ne don kare manoman ta daga masu shigo da wadannan kayakin daga ketare.

Bayan wannan sassauci da ta yi a fannin aikin noma, EU na bukatar sauran kasashe su ma su yi mata rangwame a fannonin yiwa jama´a hidima da samar da kayan masana´antu a cikin kungiyar ta WTO.

To amma duk da haka Brazil da ministan harkokin wajen ta Celso Amorim na ci-gaba da nuna taurin kai. A dai halin da ake ciki ba wata kyakkyawar alamar samun nasarar tattaunawar ta Hongkong, musamman ganin yadda aka yi ta tashi baram baram a tarukan WTO a baya sakamakon irin wadannan bukatu da kasashe ke gabatarwa.

EU na kokarin jawo kasashe masu tasowa a gareta ta hanyar ba su karin taimakon raya kasa, to amma hakan ba zai samar da wani abin a zo a gani ba domin hasali ma ba sa biyan kudin kwastan ga daukacin kayakin da suke shiga da su kasuwanin kungiyar EU.

Ko da yake Peter Mandelson ya ce zai kara matsawa Brazil lamba don hana rugujewar tattaunawar ta WTO, amma ya ce ba ya sa ran samun wani ci-gaba a taron na Hongkong.