1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kada kuri'a kan shigar Turkiya cikin EU

November 23, 2016

Majalisar dokoki ta Kungiyar Tarayyar Turai ta EU na shirin kada kuri'a kan batun amincewa ko kuma yin watsi da bukatar Turkiya ta shiga cikin Kungiyar.

Belgien Federica Mogherini im EU-Parlament in Brüssel
Hoto: DW/I. Koval

Shugaban Turkiya Racep Tayyib Erdogan ya ce kuri'ar da majalisar dokoki ta Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ke shirin kadawa dangane da dakatar da tattaunawa kan shigar kasar cikin kungiyar ba zai amfana wa Turkiya komai ba ko da kuwa sakamakon kuri'ar da za a kada ya yi wa kasar kyau. Tuni dai aka fara samun sabanin ra'ayi kan wannan batu.

Shugaba Erdogan dai ya bayyana wannan matsayi da majalisar dokokin EU din ke shirin dauka wanda a fayyace ya ke cewar za su bada goyon bayansu wajen ganin an dakatar da wannan tattaunawa, ba zai taimakawa Turkiya ta kowanne fanni ba, domin kuwa yanzu haka Ankara ta fi maida hankalinta ne wajen ganin ta sake gina kanta da ma daidaita lamuranta na cikin gida biyo bayan 'yan matsalolin da ta fuskanta a 'yan watannin da suka gabata wanda suka hada da yunkurin nan da aka yi na kifar da gwamnati da bakin bindiga.

Hoto: Picture-Alliance/dpa/S. Sunat

Erdogan din ya ce tuni suka fahimci cewar akwai kasashe da dama na EU da ke aiki ta karkashin kasa wajen ganin an dakatar da wannan tattaunawa tun ba yau ba, amma kuma a idon duniya sai su nuna cewar suna da shauki na ganin an ci gaba da zantawar da ma amincewa da  shigar da Turkiyar a kungiyar ta EU. Wannan ne ma ya sanya shugaban ya ce akwai yiwuwar nan gaba kasar ta kada kuri'ar raba gardama ta hakura da shiga EU din kana ta fuskanci magana ta shiga kungiyar nan ta Shangai Cooperation wadda Rasha da China ke zaman mambobi a cikinta.

A daura da wannan kalamai da Erdogan ke yi, wasu 'yan majalisar dokokin EU suka ce wannan zargin da ya ke na cewar wasu kasashen Turai na yi wa Ankara na shiga EU, ba shi da tushe, inda suka ce ya na wadannan kalamai domin su mamaye kafafen yada labarai da zummar ganin an mance da irin abin da ya ke aikatawa a kasarsa wanda suka saba doka ciki kuwa har da gallazawa 'yan adawa da ma hana mutane ganinsu a wuraren da ake tsare da su wanda Arne Lietz da ke zaman guda daga cikin 'yan majalisar ya ce shi shaida ne.


"Mun so zuwa gidan kaso inda ake tsare da mukaddashin jam'iyyar nan ta HDP da ke goyon bayan Kurdawa amma ba a amince mun ganshi ba saboda 'yan sanda da wasu jami'an tsaro dauke da manyan makamai sun yi mana tunga a kan hanya".

Hoto: picture alliance/AA/M. Kamaci

To sai dai duk da wannan yanayi da ake ciki da kuma ci gaba da shan suka da mahukuntan na Ankara ke yi musamman dangane da abin da wasu suka kira karya kashin bayan masu adawa da Erdogan ke yi, shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel na ganin ya kyautu a bar wasu kafofi bude wadanda za a yi amfani da su wajen ci gaba da tattaunawa da Turkiya din kan abububuwan da za su amfani bangarorin biyu.


"Ni kam zan bar kofofi bude ta zantawa da Turkiya domin kuwa akwai wasu abubuwa da muke son yi tarayya a kai da kasar, amma ya kyautu a fahimci cewar ba za mu amince da abubuwan da ke faruwa a kasar ba wanda ke da sosa rai matuka".

Da dama dai yanzu haka na zuba idanu don ganin yadda zaman majalisar dokokin EU din zai kasance kan wannan batu ko dai ba lallai ne uwar kungiyar ta amince da shi ba, inda a share guda wasu ke dakon irin matakin da shugaba Erdogan zai dauka idan sakamakon wannan zama ya fita.