1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kaddamar da makarantar horon soja

Salissou Boukari LM
October 3, 2024

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar da hadin gwiwar ma'aikatar tsaron kasar ta kaddamar da wata babbar makarantar ilimi mai zurfi ta aikin soja, wadda aka kira da makarantar horas da dubarun yaki da tsaron kasa.

Nijar | Yamai | Abdourahamane Tiani | Sojoji
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

Wannan makaranta dai, za ta horas da manyan sojoji da sauran bangare na manyan  jami'an tsaro. Jamhuriyar ta Nijar dai ta jima dauke da wannan buri na samar da wannan makaranta da za ta rage babban dogaro na manyan sojojin kasar na zuwa wasu kasashen ketare, domin samun cikamakin horo na babban soja. Kaddamar da wannan makaranta babban ci-gaba ne a fannin horo na manyan sojojin Nijar, wanda ta hanyar wannan makaranta suke samun dukkanin horon zama manyan sojoji da ake kira da Turancin Faranasa da (Officier Supérieur). A yanzu makarantar, ta buda kofofinta ga dalibai kimanin 26 da suka hada da manyan sojoji da jandarmomi da manyan jami'an da na fasa kwabri da ma manyan jami'an tsaron fararar hula na ma'aikatar cikin gida da harkokin waje. Da yake tsokaci kan wannan batu Farfesa Dicko Abdourahamane masani kan harkokin tsaro da yaki da ta'addanci ya ce, bude wannan makaranta wata babbar dama ce ga sojojin Nijar da sauran jami'an tsaron kasar. Baya ga manyan sojojin Nijar din, wannan makaranta ka iya karbar dalibai sojoji na kasashe aminanta musamman na kungiyar AES da suka hada da Nijar din da Mali da kuma Burkina Faso.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani