Shirin kaddamar da sabuwar gwamnatin Burkina Faso
February 11, 2022An tabbatar da Lt. Kanar Paul Henri Sandaogo Damiba a matsayin sabon shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Burkina Faso, a cikin wata sanarwa da kotun kula da tsarin mulkin ta bayar a wannan makon.
Sannan a wannan Jumma'a wata sanarwar sojan kasar ta tabbatar da cewa an saka ranar Laraba mai zuwa 16 ga wannan wata na Febrairu a matsayin ranar da za a yi bikin kaddamar da sabon shugaban gwamnatin mulkin sojan, bayan juyin mulkin ranar 24 ga watan Janairu da ya kawo karshen gwamnatin Shugaba Roch Marc Christian Kabore.
Kanar Damiba ya yi alkawarin samar da tsaro a kasar ta Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka wadda take fuskantar hare-hare daga kungiyoyin masu nasaba da kishin addinin Islama. Sakamakon juyin mulkin an dakatar da kasar ta Burkina Faso a kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma da kungiyar Tarayyar Afirka.