1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kaduna ta kulla yarjejeniya da kamfanin Zipline

Ramatu Garba Baba
February 3, 2021

Gwamnatin jihar Kaduna ta kulla wata yarjejeniyar da kamfanin Zipline na Amurka mai amfani da jirgin sama mara matuki a dawainiyar aika sakonni na magunguna da allurai zuwa asibitoci.

Zipline | Medikamententransport mit Drohnen
Hoto: picture-alliance/dpa/Vaccine Alliance GAVI/T. Noel

Jiragen na iya kai magungunan asibitoci ne ta hanyar amfani da manhajar GPS, ana mika kunshin magungunan ta hanyar salo irin na saukar lema, jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya na daga cikin jihohin da ta fuskanci ta'asar annobar corona inda jihar ta kasance cikin yanayi na dokar kulle a tsawon lokaci. 

Gwamnan jihar Nasir El-Rufai, ya ce matakin zai kawo saukin rayuwa ga miliyoyin al'ummar jihar a kulawa da bukatunsu musanman a fannin kiwon lafiya a wannan lokaci da ake ci gaba da yakar annobar corona.

Kamfanin na Zipline ya shahara a amfani da jiragensa marasa matuki, wajen aika kunshin sakonni zuwa cibiyoyin lafiya kamar yadda aka gani a kasashe kamar su Ghana da Ruwanda da kuma Amirka.