1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro kan matsalolin Najeriya a Kaduna

March 7, 2024

Kungiyoyin kasa da kasa da ke fafatukar samar da zaman lafiya da malaman addinai tare da sarakunan gargajiya daga jihohi 36 da ke a Tarayyar Najeriya, sun kammala taron kwanaki biyu a Kaduna.

Najeriya | Rigasa | Abuja-Kaduna | Jirgin Kasa
A bara an kai wa jirgin kasan Najeriya da ke jigilar fasinja daga Kaduna zuwa Abuja hariHoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Tun da farko dai shugaban shirya taron na Kadunan Revren Josept John Hayab daga wata kungiyar da ke kyautata fahimtar juna tsakanin mabambanta addinai a Najeriyar, ya bayyana cewa sun tattaro dukkanin masu ruwa da tsaki a bangaren samar da zaman lafiyar ne domin kara bullo da hanyoyin kyautata mu'ammala da zamantakewa tsakanin al'umma da masu ruwa da tsaki da nufin nemo bakin zaren matsaloilin rashin tsaron da ke addabar kasar.

Kaduna-cibiyar addinai a tsakiyar tarayyar Najeriya

02:28

This browser does not support the video element.

Manyan malaman addinai da kusoshin gwamnatin jihar ta Kaduna ne suka halarci taron, inda suka jaddada fa'idar da ke akwai wajen assasa yaki gadan-gadan dangane da matsalar tsaron da take neman hana kowane bangaren kasar ci-gaba. Sheikh Farfesa Khalid Aliyu Abubakar shi ne wakilin sarkin musulmi a wajen taron da ya bayyana cewa tabbatar da adalci da bai wa kowane dan kasa hakkinsa, sune hanyar kawo karshen rashin tsaron. Ya kuma janyo hankalin dukkanin masu ruwa da tsaki a kan taimakawa hukumomi da kungiyoyi da shawarwarin da suka kamata, domin daukar matakan dakile matsalaolin da suke hana ci-gaban kasar da ma al'ummarta.