1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan bindiga sun sace dalibai sama da 100

Ramatu Garba Baba
July 5, 2021

Dalibai sama da 100 'yan bindiga suka sace a safiyar wannan Litinin daga wata makarantar Sakandare ta Bethel Baptist High School a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Nigeria Hunderte Mädchen in Zamfara entführt
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Rahotanni daga jihar Kaduna da ke Najeriya, na cewa, 'yan bindiga sun sace dalibai sama da dari ne daga wata makarantar Sakandare mai suna Bethel Baptist. Yan bindigan, sun kai harin makarantar, da safiyar wannan Litinin kamar yadda wani mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Mohammed Jalige ya tabbatar. 

Jami'in bai yi karin bayani kan alkaluman daliban da aka yi awon gaba da su ba, sai dai daya daga cikin malaman makarantar, Emmanuel Paul, ya ce dalibai kimanin dari da hamsin 'yan bindigan suka kama amma ashirin da biyar daga cikinsu suka kubuce daga hannunsu. Wannan na zuwa ne kwana guda da sace wasu mutane daga wani asibitin kutare da 'yan bindigan suka yi a jihar da ke yakin arewacin Najeriya.