1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafa gwamnatin wucin gadi a Libiya

July 10, 2011

Majalisar Ɗinkin Duniya ta tura manzo na musamman zuwa Libiya domin lalubo hanyoyin warware rikicin ƙasar ta hanyar siyasa ta kafa majalisar wucin gadi

Mata masu samun horo a Tripoli domin yi wa Gadhafi yaƙiHoto: dapd

Wata sanarwa daga ofishin sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Ban Ki Moon ta bayyana cewar wani manzon da majalisar ta tura ƙasar Libiya ya tattauna tare da firaministan da kuma ministan kula da harkokin wajen ƙasar game da buƙatar samar da majalisar wucin gadin da za ta tafiyar da al'amura a ƙasar. Sanarwar, wadda aka fitar a wannan Lahadin 10 ga watan Juli ta ce manzon sakatare janar ɗin, Abdul Elah al-Khatib, ya gana da firaminista Al-Baghdadi Ali Al-Mahmoudi da kuma Abdelati Obeidi a birnin Tripoli, inda ya bayyana buƙatar warware rikicin na ƙasar Libiya a siyasance domin kauce wa yanayin ƙara jefa al'ummar Libiya cikin uƙuba da kuma biyan buƙatunsu na bin tafarkin dimoƙraɗiyya a nan gaba.

Hakanan sanarwar ta ce wakilin sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniyar ya kuma saurari ra'ayin hukumomin Libiya game da tasirin takunkumin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya wa ƙasar da kuma hare-haren da ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO ke ƙaddamarwa akan Libiya a ƙarƙashin wani ƙudiri na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya tanadi kare fararen hula- waɗanda kuma shugaba Mouamer Gadhafi ya kwatanta da cewar wani sabon nau'i ne na mulkin mallakar da ke da nufin satar man fetur da Allah ya hore wa ƙasarsa.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Halima Balaraba Abbas